Posts

Showing posts from April, 2026

Abin damuwa ne yadda gwamnatin Najeriya ke ci gaba da cin bashi duk da cire tallafin mai- Sarkin Kano Sunusi

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya bayyana damuwarsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da dogaro da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur. Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na News Central TV da Hausa Daily Times ta kalla a ranar Jumma’a, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya yi gargaɗin cewa raunin tsare-tsaren kula da harkokin kuɗi na iya lalata ribar da ake sa ran samu daga sabbin sauye-sauyen tattalin arziƙi. Sanusi, wanda ya daɗe yana sukar tsarin tallafin mai, ya sake jaddada cewa tsarin ba zai dore ba, yana mai sukar yadda ƙasar ta dogara da matatun mai na ƙasashen waje duk da cewa na cikin gida ba a amfani da su yadda ya kamata. Duk da goyon bayansa ga sabon tsarin manufofin tattalin arziƙin Najeriya da ya ce an samu gagarumin sauyi, tsohon gwamnan na CBN ya yi tambaya kan yadda aka tsara aiwatar da sauye-sauyen, musamman cire tallafin mai da kuma ‘yantar da kasuwar canjin kuɗi. Ya ƙara da cewa aiwatar da irin waɗannan matakai a yanayin da manufo...
Image
  Tinubu Ya Nemi Sabon Rancen $516m Domin Gina Babbar Hanyar Sokoto–Badagry. A wani mataki da ke jan hankalin ‘yan ƙasa da masu bibiyar tattalin arziki, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon rancen dala miliyan $516.3 daga Bankin Jamus (Deutsche Bank). Wannan kuɗi zai taimaka wajen aiwatar da wasu muhimman sassa na aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry—wani gagarumin shiri da ake kallon zai sauya yanayin sufuri a ƙasar. Wasiƙar da shugaban ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zauren majalisa, ta bayyana cewa aikin na cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin wajen inganta hanyoyin sadarwa da bunƙasa tattalin arziki. Hanyar mai tsawon kusan kilomita 1,000 za ta haɗa yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, ta hanyar sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki da mutane cikin sauri da aminci. Bayanai sun nuna cewa wannan hanya za ta fara ne daga Illela a jihar Sokoto, ta ratsa jihohin Kebbi, Niger, Kwara, Oyo...
Image
KO KUN SAN DAN TAKARAN DA ZA A TSAYAR TAKARAR GOMNAN JIHAR YOBE A JAM'IYYAR APC?    A daidai lokacin da al'umar jihar yobe ke ta kiraye-kiraye daga bangarori mabanbanta a jihar yobe domin samun dan takaran da suke so a tsayar musu a jam'iyyar APC kan al'ummar jihar ya rabu zuwa kaso mabanbanta, inda mafiya shaharar bangarorin suka kasance guda hudu. bangarorin sun haɗa da: 1. bangaren magoya bayan sanata Mohammed Bomoi. 2.  bangare na biyu sune magoya bayan sanata Ahmed Ibrahim Lawan. 3. Bangare na uku sune magoya bayan Barista Kashim Musa Tumsa. 4. Bangare na hudu sune bangaren magoya bayan honarabul Baba Malam Wali. wadannan sune ƴan takara mafiya shahara da sanuwa da kuma karfin siyasa a jihar yobe, wanda hakan yasa ake ganin dole ne indai jam'iyyar APC na jihar yobe zata tsayar da dan takarar gwamna to wajibin ta ne ta tsayar da ɗaya cikin huɗun nan. Bisa ga hasashe muna bukatar ku bayyana ra'ayoyin ku akan wanda kuka fi sa ran zai zama magajin Gwamnatin jih...

Za a mayar da sauraron shari'ar Sheikh Abduljabbar karkarshin kotun gwamnatin tarayya

 Kotun daukaka kara dake Kano ta mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasir Kabara zuwa ofishin babbar mai shari’a ta jihar, domin mayar da shari'ar karkashin kulawar kotun tarayya. Rahotanni sun nuna cewa a zaman kotun da aka yi na ranar Alhamis, 23 ga Afrilu 2026, Abduljabbar ya bayyana cewa zai kare kansa da kansa ba tare da lauya ba. A bangaren gwamnatin jihar Kano kuwa, lauyoyin ta sun bukaci a yi watsi da karar da ya daukaka, suna masu cewa akwai kura-kurai a cikin takardun da aka gabatar. Kotun ta jaddada cewa doka ta ba shi damar kare kansa ko kuma ya nada lauya, sannan ta ce babu wani hukunci da aka yanke tukuna a kan wannan daukaka kara. Daga karshe, kotun ta lura da cewa takardun da bangarorin suka gabatar ba su cika ka’ida ba, don haka ta mayar da shari’ar zuwa ofishin babbar mai shari’a ta jihar domin a mayar da ita kotun ƙasa, ta yadda za a ci gaba da shari’ar cikin adalci.

Hukumar zaben ta kasa INEC ta bude damar yin zabukan fitar da gwani ga jam'iyyu

 Jadawalin zaɓen 2027 ya fara daga yau inda hukumar zabe ta kasa INEC ta bude wa’adin kwanaki 38 ga jam’iyyun siyasa domin gudanar da zaben fitar da gwani. Daga yau 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, jam’iyyun siyasa za su gudanar da fitar da gwani na mukaman shugaban kasa, gwamna, yan majalisar dokoki ta kasa da na jihohi, tare da warware duk wata takaddama da ka iya tasowa. Haka kuma, an umarci jam’iyyun da su mika rajistar mambobinsu ga INEC akalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani, yayin da ranar 10 ga Mayu, 2026 ta kasance ranar karshe na mika wadannan bayanai.

Hukumar tsaron kasa (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai

 Hukumar Tsaron Kasa (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, bisa zargin kutse cikin tattaunawar waya ta mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA), Nuhu Ribadu.   Tsohon ministan babban birnin tarayya (FCT) yana fuskantar tuhuma mai dauke da maki biyar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.   A zaman kotun na Alhamis, lauyan gwamnati ya sanar da cewa an sabunta tuhumar daga maki uku zuwa biyar. Saboda haka, mai shari’a Joyce Abdulmalik ta soke tuhumar da ta gabata.   El-Rufai ya musanta dukkan tuhumar da aka gabatar masa. Bayan haka, lauyan DSS, Oluwole Aladeloye, ya nemi kotu ta ware kwanakin shari’a.   Sai dai lauyan el-Rufai, Oluwole Iyamu, ya yi adawa da bukatar, inda ya ce yana bukatar tattaunawa da abokinsa na shari’a saboda ya shafe lokaci a hannun hukumomin tsaro daban-daban.

Gwamnan Jihar Yobe, Dr. Mai Mala Buni, Ya Yi Godiya Ga Al’ummar Jihar Yobe, Ya Yi Kira Da A Ci Gaba Da Zaman Lafiya

Mai girma Gwamnan Jihar Yobe, Dr. Mai Mala Buni, ya bayyana godiya mai zurfi ga al’ummar jihar bisa goyon baya da ƙauna da suka nuna masa tun daga lokacin da ya hau kujerar mulki.   A cikin saƙonsa, Gwamnan ya ce:   “Na ke turo muku wannan saƙo ne da zuciya cike da godiya mai zurfi. Tun daga ranar da na ɗauki nauyin jagorantar jiharmu a matsayin Gwamna, ban ga komai daga gare ku ba sai aminci, girmamawa da ƙauna ta gaskiya. Goɗiyarku ita ce tubalin nasarorin da muka cimma tare, kuma ina yaba muku yadda kuka rayu cikin amana da zaman lafiya.”   Mai Mala Buni ya kuma yi nuni da cewa yayin da ake kusantar shekarar 2027, ana ci gaba da tattaunawa kan wanda zai gaje shi a matsayin Gwamna. Sai dai ya jaddada cewa wannan lamari na nan a hannun Allah, domin Shi ne ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya zaɓa.   Ya ce:   “Kowa ya ɗauki darasi daga labarina. Mulki da iko na Allah ne kaɗai. Shi ne yake ba da jagoranci ga wanda Ya so, a lokaci...

HAJJI 2026: za a fara jigilar alhazai Najeriya zuwa kasa mai tsarki ranar 3 ga Mayu

Ana sa ran Najeriya za ta fara jigilar maniyyata zuwa ƙasar Saudiyya domin Hajjin 2026 daga ranar 3 ga Mayu, wanda zai nuna fara jigilar alhazai daga ƙasar. Kafin fara jigilar, ana sa ran wata tawagar ma'aikata ta musamman za ta tashi a ranar 27 ga Afrilu domin kammala muhimman shirye-shirye kamar masauki, abinci da kuma harkokin lafiya ga alhazan Najeriya. Hukumar NAHCON ce za ta jagoranci wannan aiki domin tabbatar da tafiyar Hajji cikin tsari da nasara.