KO KUN SAN DAN TAKARAN DA ZA A TSAYAR TAKARAR GOMNAN JIHAR YOBE A JAM'IYYAR APC?
A daidai lokacin da al'umar jihar yobe ke ta kiraye-kiraye daga bangarori mabanbanta a jihar yobe domin samun dan takaran da suke so a tsayar musu a jam'iyyar APC kan al'ummar jihar ya rabu zuwa kaso mabanbanta, inda mafiya shaharar bangarorin suka kasance guda hudu.
bangarorin sun haɗa da:
1. bangaren magoya bayan sanata Mohammed Bomoi.
2. bangare na biyu sune magoya bayan sanata Ahmed Ibrahim Lawan.
3. Bangare na uku sune magoya bayan Barista Kashim Musa Tumsa.
4. Bangare na hudu sune bangaren magoya bayan honarabul Baba Malam Wali.
wadannan sune ƴan takara mafiya shahara da sanuwa da kuma karfin siyasa a jihar yobe, wanda hakan yasa ake ganin dole ne indai jam'iyyar APC na jihar yobe zata tsayar da dan takarar gwamna to wajibin ta ne ta tsayar da ɗaya cikin huɗun nan.
Bisa ga hasashe muna bukatar ku bayyana ra'ayoyin ku akan wanda kuka fi sa ran zai zama magajin Gwamnatin jihar yobe?
zamu zo muku da cikakken rahoto da sahihin bayani kan makomar magajin Gwamnatin jihar yobe nan ba da jimawa ba.

Comments
Post a Comment