Za a mayar da sauraron shari'ar Sheikh Abduljabbar karkarshin kotun gwamnatin tarayya
Kotun daukaka kara dake Kano ta mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasir Kabara zuwa ofishin babbar mai shari’a ta jihar, domin mayar da shari'ar karkashin kulawar kotun tarayya.
Rahotanni sun nuna cewa a zaman kotun da aka yi na ranar Alhamis, 23 ga Afrilu 2026, Abduljabbar ya bayyana cewa zai kare kansa da kansa ba tare da lauya ba.
A bangaren gwamnatin jihar Kano kuwa, lauyoyin ta sun bukaci a yi watsi da karar da ya daukaka, suna masu cewa akwai kura-kurai a cikin takardun da aka gabatar.
Kotun ta jaddada cewa doka ta ba shi damar kare kansa ko kuma ya nada lauya, sannan ta ce babu wani hukunci da aka yanke tukuna a kan wannan daukaka kara.
Daga karshe, kotun ta lura da cewa takardun da bangarorin suka gabatar ba su cika ka’ida ba, don haka ta mayar da shari’ar zuwa ofishin babbar mai shari’a ta jihar domin a mayar da ita kotun ƙasa, ta yadda za a ci gaba da shari’ar cikin adalci.
Comments
Post a Comment