Abin damuwa ne yadda gwamnatin Najeriya ke ci gaba da cin bashi duk da cire tallafin mai- Sarkin Kano Sunusi
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya bayyana damuwarsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da dogaro da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na News Central TV da Hausa Daily Times ta kalla a ranar Jumma’a, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya yi gargaɗin cewa raunin tsare-tsaren kula da harkokin kuɗi na iya lalata ribar da ake sa ran samu daga sabbin sauye-sauyen tattalin arziƙi.
Sanusi, wanda ya daɗe yana sukar tsarin tallafin mai, ya sake jaddada cewa tsarin ba zai dore ba, yana mai sukar yadda ƙasar ta dogara da matatun mai na ƙasashen waje duk da cewa na cikin gida ba a amfani da su yadda ya kamata.
Duk da goyon bayansa ga sabon tsarin manufofin tattalin arziƙin Najeriya da ya ce an samu gagarumin sauyi, tsohon gwamnan na CBN ya yi tambaya kan yadda aka tsara aiwatar da sauye-sauyen, musamman cire tallafin mai da kuma ‘yantar da kasuwar canjin kuɗi.
Ya ƙara da cewa aiwatar da irin waɗannan matakai a yanayin da manufofin kuɗi ba su da tsauri ya taimaka wajen janyo faɗuwar darajar naira cikin sauri a yanzu.
Comments
Post a Comment