Hukumar zaben ta kasa INEC ta bude damar yin zabukan fitar da gwani ga jam'iyyu
Jadawalin zaɓen 2027 ya fara daga yau inda hukumar zabe ta kasa INEC ta bude wa’adin kwanaki 38 ga jam’iyyun siyasa domin gudanar da zaben fitar da gwani.
Daga yau 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, jam’iyyun siyasa za su gudanar da fitar da gwani na mukaman shugaban kasa, gwamna, yan majalisar dokoki ta kasa da na jihohi, tare da warware duk wata takaddama da ka iya tasowa.
Haka kuma, an umarci jam’iyyun da su mika rajistar mambobinsu ga INEC akalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani, yayin da ranar 10 ga Mayu, 2026 ta kasance ranar karshe na mika wadannan bayanai.
masha Allah
ReplyDelete